Posts

AURE RIBAR MASOYA

🥰 ƘASIDA GAME DA AURE 🥰  [ Amshi ]  Ƙarshen maganar so dai ayo aure ribar masoya Daɗi na zumar so sai cikin aure in har tsakani akwai ƙauna (1)  Allah Mabuwayi Mai yawan kyauta Mai bada baiwa Sunanka nasa farko Ka lamince kar in gazawa Don banida mai tama ni in miƙe ba karkacewa Sai Kai Ma'ishin Sarki ina fatan yaa Rabbi Ka amsa roƙo na (2) Bana iya gegewa a waƙe sai nayo salati Ga Muhammadu Manzo Annabin tsira Abba ga Fati Na sanya sahabbai har iyalai tsarkaka a baiti  Na sa mabiya dominko bana tsame wanda ke binsa Manzo na (3) Mun wayi gari ranar biki ƙanne harma da yayye Dangi duka sunzo ga sahun ƴaƴa sannan iyaye Taro na abokai ɓangaren mata suko ƙawaye Kowa fara'a an ɗaura auren soyayya a yau mu muna murna (4)  Allah a cikin tsarinsa dama yace ya ƙawata  Wa maza sha'awar ƙauna da soyayya tsantsa ga mata Sannan ya nufa aure ya zamto hanyar daƙile ta Hanya ɗaya tilo wacce kowa ke fatan a sunansa an zana  (5) Aure ya zamo ƙauna da soyayya sune sil...

IDAN ƁERA NADA SATA..

Image
  JAGORA DA WANDA AKE JAGORANTA   Allah maɗaukakin sarki ya raba ayyuka kuma yaba kowa nasa: 1- Shuwagabanni su riƙe nasu suyi ƙoƙarin saukewa, domin Allah zai tambayesu game da nauyin da ya dora masu.  2- Waɗanda ake shugabanta suma su riƙe nasu kuma suyi ƙoƙarin saukewa, domin babu shakka za'a tambayesu game da haƙƙoƙin shuwagabanninsu da aka ɗora masu.  Kada wani ya shiga aikin wani!  Duk wanda ya shiga aikin wani, ko yayi sakaci wajen zartar da nasa aikin, lallai ya saɓawa Allah maɗaukakin sarki. Shugabanci abune mai tsananin wahala, kuma lallai akwai hisabi tsakanin shuwagabanni da mabiya.  Duk wani shugaba wanda yayi amfani da jagorancinsa ko ƙarfin mulkinsa ya muzgunawa waɗanda yake jagoranta, lallai zai tarar da hukuncinsa a wajen ubangijinsa.  Tabbas haƙƙi ne ga shugaba ya tsarewa al'ummarsa ababe kamar haka:   (1) Rayukansu   (2) Addininsu  (3) Dukiyoyinsu  (4) Hankulansu   (5) Mutuncinsu Da sauransu. ...

KU YAƊA ALKHAIRI A TSAKANINKU

Image
  LALLAI KUYI UMARNI DA KYAKKYAWA DA KUMA HANI DAGA MUMMUNA  Wajibi ne ga duk wani musulmi wanda ya sami dama da iko, yayi umarni da kyakkyawa da hani daga mummuna musamman ga abinda ya bayyana gareshi. Lallai akwai buƙatar ya natsu cikin hakan wajen amfani da ƙa'idoji da matakai na shari'ah, wato kamar: - ILIMI  - HAQURI  - TAUSASAWA GWARGWADON IKO  - JURIYA GA CUTARWA  - LURA DA MASLAHA DA KISHIYARTA  Da sauransu.  Duk waɗannan zasu afkune sakamakon faɗin ma'aiki-tsira da aminci su ƙara tabbata gareshi-inda yake cewa-: “ DUK WANDA YAGA WANI ABIN ƘI DAGA CIKINKU TO YA CANZASHI DA HANNUNSA, IDAN BAZAI IYA BA SAI YA CANZA DA BAKINSA, IDAN BAZAI IYA BA SAI YA KYAMACESHI DA ZUCIYARSA, WANNAN SHINE MAFI RAUNIN IMANI ” Allah ya bamu ikon fa'idantuwa daga matakan, da kuma ikon gudanar dasu. ✍🏻  Abul-Mustapha Al-athary  June 11, 2015

TA'AZIYYAR SHEIKH LUHAYDAAN

Image
Qasidah cikin tsarin :                   ARAUSA         •┈┈•┈┈•⊰✿🌺✿⊱•┈┈•┈┈•    Mai taken :     Ta'aziyyar Sheikh Luhaydaan                             😭😭😭 (1) Mun zam cikin damuwa ƙwarai da  ahzaanu         akan rashin gwarzon malami Luhaydaanu (2) Wannan da zargin mai zargi baya yin tasiri        akansa balle baƙin hali na fattaanu (3) Wajen nasiha yana yinta cikin hikima        ya fayyace gaskiya tsantsa ga insaanu (4) Gwani kafaffe akan bin magabata wajen        riƙo ga Sunnah da bibiya ga Qur'anu (5) Sam baya yarda da tsunbure cikin manhaji         koko kafar yaɗa ayyuka na shaiɗanu  (6) Ya sami ƙauna da karɓuwa wajen talikai         ba ko kuɗi ba mulki irin na sulɗaanu  (7)...

MARTANI GA KUNGIYAR AFENIFERE DA SAHARA REPORTERS

Image
                👇              AMSHI : Sahara Reporters ƴan tsiya    Jaridar marassa tarbiya  Basa son a zauna lafiya       ┈┉┅━❀🍃🌺🍃❀━┅┉┈        Da sunanka Allah kai ɗaya  Maƙagi gwani  mai  duniya  Gama da ƙasashen nahiya     Damu talikan Najeriya  Salati  kayo  gun  Mursali Abinso ga duk mai hankali  Ba mai ja dashi sai Jahili  Koma baya jikan tinkiya  Na ɗau ɗamara in saliɓe     Taron kafirai zan kakkaɓe     In yo martani ba shaguɓe   Ga gungun marassa tarbiya Yarbawa ku buɗe kunnuwa  Zan ɗan baku saƙo ba yawa Ku ɗauka ku kai gun ƴan uwa Musamman na waccan ƙungiya  Mai son yin ƙabilanci yayo  Mai son ɓangaranci je kayo     Kubar  masu  addini  suyo    Shi zai sa a wanye lafiya Musulmai munason lalama...

ENGAUSA mai taken : GOMAN FARKO NA ZHUL-HIJJAH

Image
Sai nake cewa : (1) Da sunan rabbi zan tsaro      batu ga introduction (2) A farko ambaton sarki     gwani mai bada direction (3) Halitta, mallaka, shi'dai    yake jujjuya condition (4) Kadaitaccen abin bautar    da bai yarda amai portion (5) Ka aiko annabin 'karshe     yazo don bada formation (6) Salati rabbi 'kara mai     yakai 'karshen promotion (7) Sahabbai har iyalai na-      -sa duk sanya a summation (8) Anan zanzo da zance don      nufin samar da solution (9) Ilaahy yai dare domin       yazam munyo relaxation (10) Ma'kagin wanda yai rana      ya sanya taita yin motion (11) Yasa kwanan wata sauri     gaban rana wajen action (12) Watanni gun gwanin sarki     twelve ne babu temptation (13) Watan 'karshe na zhul-hijja     nake sauri ...

NA FITO YAWO GABAGAƊI..

Image
  Akan harshen         ABDUL-JABBAR             ( shugaban ƴan kogo ) :                     👇                👇 Na fito yawo gabagaɗi                gashi an rarraunatani  Ca nake a cikin garin nan              ni kaɗai zan ruɗa birni Na zata a fagen karatu            babu mai iya tsorata ni Sai nazo na zaƙe ina ku-                   -ri ina neman a bini Nayi alfahari ga ƴan ko-    -gonmu sai suka zuzzugani To ashe wasu basu bacci       sun shiri don murƙushe ni Na zamo tamkar barewa            zakuna sun kewaye ni Gashi na ɗebo ruwa ma-         -'ishi da za'a tafarfasa ni Na riga na furta manyan    ...