ENGAUSA mai taken : GOMAN FARKO NA ZHUL-HIJJAH
Sai nake cewa :
(1)
Da sunan rabbi zan tsaro
batu ga introduction
(2)
A farko ambaton sarki
gwani mai bada direction
(3)
Halitta, mallaka, shi'dai
yake jujjuya condition
(4)
Kadaitaccen abin bautar
da bai yarda amai portion
(5)
Ka aiko annabin 'karshe
yazo don bada formation
(6)
Salati rabbi 'kara mai
yakai 'karshen promotion
(7)
Sahabbai har iyalai na-
-sa duk sanya a summation
(8)
Anan zanzo da zance don
nufin samar da solution
(9)
Ilaahy yai dare domin
yazam munyo relaxation
(10)
Ma'kagin wanda yai rana
ya sanya taita yin motion
(11)
Yasa kwanan wata sauri
gaban rana wajen action
(12)
Watanni gun gwanin sarki
twelve ne babu temptation
(13)
Watan 'karshe na zhul-hijja
nake sauri nayo mention
(14)
Watan ya tara alkhairan
da kowa keda ambition
(15)
A kwana goma tun farkon
watan mun samu induction
(16)
Ibadu zamuyo sam kar-
-musa wargi da exhaustion
(17)
Na sallar nafiloli ko
muyo Qur'an recitation
(18)
Muyo fasting mu'dau har-
-kar zumunci as tradition
(19)
Cikin tsarin ciyarwa do-
-le sai munyo reformation
(20)
Hawan arfa a ranar za-
-mu 'dau fasting na devotion
(21)
Ga mai aikin haji shi gun-
-sa rana ce ta injunction
(22)
Tsayawa zai a fili don
ganin ya yo transaction
(23)
A ranar goma idi za
muje bayan decoration
(24)
A fili za muyo sallah
muna d'an exclamation
(25)
Da zarar mun idar yanka
muke hange a intention
(26)
Da rago yafi lada don
hakan manzo yayo mention
(27)
Akan harkar bikin sallah
fa sai mun 'danyi correction
(28)
Zuwa idi na kowane
abun sam babu exception
(29)
Maza, mata da yara 'kan-
-'kana in maximization
(30)
Da mata masu aure har-
-da yan mata cikin action
(31)
Da mai haila da mai bi'ki
kuje kuma kuyo function
(32)
Kuyo kallo na alkhairai
cikin tsantsar delectation
(33)
Hijabi zakusa domin
yazam an sami partition
(34)
Fitowa ba hijabi ai-
-bu ne tsantsa da violation
(35)
Mu koma kan batun gayu
mu tsinkayar dasu caution
36)
Subar party, smoking sai
mu'dan samar da conjunction
(37)
Susan cewa akwai ranar
da ba mai 'ketare sanction
(38)
Suna cutar da al'umma
ta hanyar vandalization
(39)
Da shan wiwi da shan taba
suna haifar da pollution
(40)
Allah nake ro'ko yasa wa'kar
ta d'an sassauya formation
(41)
Anan zan dan tsaya ko zai-
-fi dadin motsa emotion
✍🏻
༻📜༺
Abul-Mustapha Al-athary
═══ ༻🕸️༺═══
6/8/2019
Ku kasance tare damu a :
👇🏻
👇🏻
👇🏻
Telegram:
https://t.me/alatharytv
YouTube:
https://www.youtube.com/channel/UCFXgXP3MN525l5h5BKXMusA
Facebook:
Al-athary Tv
Call/WhatsApp:
08037894111
Website:
http://alatharytv.blogspot.com

Comments
Post a Comment