NA FITO YAWO GABAGAƊI..
Akan harshen
ABDUL-JABBAR
( shugaban ƴan kogo ) :
👇
👇
Na fito yawo gabagaɗi
gashi an rarraunatani
Ca nake a cikin garin nan
ni kaɗai zan ruɗa birni
Na zata a fagen karatu
babu mai iya tsorata ni
Sai nazo na zaƙe ina ku-
-ri ina neman a bini
Nayi alfahari ga ƴan ko-
-gonmu sai suka zuzzugani
To ashe wasu basu bacci
sun shiri don murƙushe ni
Na zamo tamkar barewa
zakuna sun kewaye ni
Gashi na ɗebo ruwa ma-
-'ishi da za'a tafarfasa ni
Na riga na furta manyan
zantukan ɓarna na muni
Duk abinda nazo dashi nan
take sai an warware ni
Gashi manyan malamai sun
kauda kai ba mai kulani
Ni ko naso ne su tanka
don yazam mun goge raini
To ashe sun gane wayon
shi yasa suka ƙaurace ni
Kan sani suka sa ido don
bada damar markaɗe ni
Sai sukai izini ga yara
gashi nan sun tarwatsa ni
Duk gari an gane shi'an-
-ci nake ƙaunar ayo ni
Na zamo wata mujiya gun
duk mutan ƙauye da birni
Na tuno ranar da Al-qa-
-sim Hotoro ya sargafe ni
Nai zufa kuma har ciki na
ya kaɗa duk nayi rauni
Sai da ƙyar fa nayo dabara
har na zuƙe mai ya barni
Shi ko Rabi'u Rijiyar le-
-mu haƙiƙa ya ƙureni
Shi waya ya kira ni rannan
gaskiya ya girmama ni
Sai ya nemi muzo a zauna
to a nan ya razana ni
Don ko in akayo zama ko
shi kaɗai zai dammare ni
Nan nayo masa ƴan dabaru
kun sani wayo gare ni
Nai jiɓin goshi a ran nan
don ko ya manmangare ni
Sai Kabiru kamar da wasa
shi kaɗai ya addabe ni
Gashi yaro ɗanye-ɗanye
sai ya rusa min tunani
Duk batun da nayo yaji ni
gobe sai ya kwalkwale ni
In akwai magana nace ai
babu sai ya ƙaryata ni
In nace da akwai yazamto
babu sai ya fallasa ni
Gashi duk zancensa sai ya-
-zo da hujjojin yaqini
Ni yawan bin dindiginsa
shi yake ɗan harzuƙa ni
Da zato na duk ƙasar nan
babu mai iya jijjiga ni
Gashi har Ganduje yau ya
sanya ɗambar daƙile ni
Ga sanarwa ta fito an
sanya ranar turbuɗe ni
Banda ƴan kogo tsiraru
masu sanya min sukuni
Ko cikin ƙwaryar gidanmu
babu ma mai bajjala ni
Sai fa ƴan Shi'ar Kano su-
-ne suke son ingiza ni
Ga Iran na miƙa ƙoƙo
har ila yau babu auni
Na zata ai zasu aiko
tallafi don ƙarfafa ni
Yanzu menene makoma
-ta ga ƴan ƙauye da birni
Nayi ɓarna ba tunanin
inda ɓarnar zata kaini
Shawara kowa ya bani
ko akwai hanyar azani
Na fito yawo gabagaɗi
gashi an rarraunata ni
✍🏻
༻📜༺
Abul-Mustapha Al-athary
═══ ༻🕸️༺═══
Ku kasance tare damu a :
👇🏻
👇🏻
👇🏻
Telegram:
https://t.me/alatharytv
YouTube:
https:// www.youtube.com/channel/UCFXgXP3MN525l5h5BKXMusA
Facebook:
Al-athary Tv
Call/WhatsApp:
08037894111
Website:
http://alatharytv.blogspot.com

Comments
Post a Comment