AURE RIBAR MASOYA

🥰 ƘASIDA GAME DA AURE 🥰

 [ Amshi

Ƙarshen maganar so dai ayo aure ribar masoya

Daɗi na zumar so sai cikin aure in har tsakani akwai ƙauna

(1) 

Allah Mabuwayi Mai yawan kyauta Mai bada baiwa

Sunanka nasa farko Ka lamince kar in gazawa

Don banida mai tama ni in miƙe ba karkacewa

Sai Kai Ma'ishin Sarki ina fatan yaa Rabbi Ka amsa roƙo na

(2)

Bana iya gegewa a waƙe sai nayo salati

Ga Muhammadu Manzo Annabin tsira Abba ga Fati

Na sanya sahabbai har iyalai tsarkaka a baiti 

Na sa mabiya dominko bana tsame wanda ke binsa Manzo na

(3)

Mun wayi gari ranar biki ƙanne harma da yayye

Dangi duka sunzo ga sahun ƴaƴa sannan iyaye

Taro na abokai ɓangaren mata suko ƙawaye

Kowa fara'a an ɗaura auren soyayya a yau mu muna murna

(4) 

Allah a cikin tsarinsa dama yace ya ƙawata 

Wa maza sha'awar ƙauna da soyayya tsantsa ga mata

Sannan ya nufa aure ya zamto hanyar daƙile ta

Hanya ɗaya tilo wacce kowa ke fatan a sunansa an zana 

(5)

Aure ya zamo ƙauna da soyayya sune silarsa 

Sannan ya zamo an sanya addini ne ginshiqinsa

Sannan kuma ga tsantsar fahimtar juna ƙarƙashinsa 

Nan za kaga daddaɗan zama mai riba babu zance na ban kwana 

(6)

Allahu Gwani ya ƙirƙiro mata domin maza ne

Domin natsuwar ɗa sai ta hanyar mataye mu gane 

A tsakani soyayya da jin tausai su garkuwa ne 

Lallai fa akwai aya cikin wannan tsari idan munbi mun auna 

(7)

Aure ni'ima sannan ga bayin Allah garkuwa ne 

Hanyar da katangaggu suke zaɓa domin riƙo ne

Don yaɗa tsatson kirki cikin ɗinbin taron mutane

Domin su zamo ƴaƴan da Manzo zai sanya a taron da zai nuna

(8)

Zan ɗanyi nasihata ga angwaye sannan amare 

Kuyi mai yiwuwa domin rufe sirrin juna a tare 

Haƙuri da kawaici ya zamo tilas ba ware-ware

In kun riƙe wannan kunbi tsarin cin ribar zama ba gudun juna 

(9)

Aure fa ibadah ne idan mun gane babu wasa 

Sai mun riƙe linzami da kyau don samun dawwamarsa

Mu sani kuma Allah zai yi sakayya ƙarshe akansa 

Da wuta yakayi koko idan munyo me kyau ya saka da aljannah

(10) 

In har kayi aure to kasan girma yazo gareka 

Kiwo na amaryar taka ya komo yau ƙarƙashinka 

Ran gobe ƙiyama kansa Allah sai ya tambayeka 

Yaya ka gudanar kayi adalci ko ka zamo shugaban ɓarna

(11)

Aure fa idan kayoshi shikenan ka ɗaure kanka

Kai keda salo tsari da hanyoyin samar da doka 

A gidanka idan ka kasa yin wannan ka ɓata harka 

In har matsala tazo kasan dai kaine zuciya zata sha ƙuna

(12)

Mata ki sani kema tulin haƙƙoƙi ne a kanki 

Aiki na miji shine fa jagora kullum na aiki 

Saidai fa ibadah wacce ta zarce komai a ɗaki 

In kin riƙe wannan Jalla zai kawo ɗaukin da ke zaki amfana

(13)

Ke karɓi batu na shi gidan aure ai dausayi ne 

Ki riƙe da kula ɗakin miji taskar ɗibar rabo ne 

In kinyi sake zakiy asara mai girma ki gane 

Duk wanda ya yayo shuka na sharri ƙarshe dole zai girbi mummuna

(14)

 Zan kulle batu ba don gazawa koko gundura ba

Sai don na taƙaice zantuka ba sai na ɗawwala ba

Ba zan hana ɗimbin masu bi jin daɗin ƙafiya ba

Saidai fa ina son fayyace daɗin aure ga duk wanda ke bi na

(15) 

Mai bi da kula nine Sulaiman Abban Mustaphan nan

Ɗa gun Uthman ango ga Maryam ƴar Bunkure ɗin nan

Mai yin nazari don miƙa saƙonni gun al'ummar nan

Shi ke ta du'a'i Rabbi sa gwauraye har tuzurai su san ƙauna

                        ✍🏻

 Abul-Mustapha Al-athary 

  24/6/1444h 🔄 17/1/2023m

Comments

Popular posts from this blog

NA FITO YAWO GABAGAƊI..

ما يثمر المنهج السلفي في المتمسّكين به

MARTANI GA KUNGIYAR AFENIFERE DA SAHARA REPORTERS