KU YAƊA ALKHAIRI A TSAKANINKU
LALLAI KUYI UMARNI DA KYAKKYAWA DA KUMA HANI DAGA MUMMUNA
Wajibi ne ga duk wani musulmi wanda ya sami dama da iko, yayi umarni da kyakkyawa da hani daga mummuna musamman ga abinda ya bayyana gareshi.
Lallai akwai buƙatar ya natsu cikin hakan wajen amfani da ƙa'idoji da matakai na shari'ah, wato kamar:
- ILIMI
- HAQURI
- TAUSASAWA GWARGWADON IKO
- JURIYA GA CUTARWA
- LURA DA MASLAHA DA KISHIYARTA
Da sauransu.
Duk waɗannan zasu afkune sakamakon faɗin ma'aiki-tsira da aminci su ƙara tabbata gareshi-inda yake cewa-:
“ DUK WANDA YAGA WANI ABIN ƘI DAGA CIKINKU TO YA CANZASHI DA HANNUNSA, IDAN BAZAI IYA BA SAI YA CANZA DA BAKINSA, IDAN BAZAI IYA BA SAI YA KYAMACESHI DA ZUCIYARSA, WANNAN SHINE MAFI RAUNIN IMANI ”
Allah ya bamu ikon fa'idantuwa daga matakan, da kuma ikon gudanar dasu.
✍🏻
Abul-Mustapha Al-athary
June 11, 2015

Comments
Post a Comment