MARTANI GA KUNGIYAR AFENIFERE DA SAHARA REPORTERS
👇
AMSHI :
Sahara Reporters ƴan tsiya
Jaridar marassa tarbiya
Basa son a zauna lafiya
┈┉┅━❀🍃🌺🍃❀━┅┉┈
Da sunanka Allah kai ɗaya
Maƙagi gwani mai duniya
Gama da ƙasashen nahiya
Damu talikan Najeriya
Salati kayo gun Mursali
Abinso ga duk mai hankali
Ba mai ja dashi sai Jahili
Koma baya jikan tinkiya
Na ɗau ɗamara in saliɓe
Taron kafirai zan kakkaɓe
In yo martani ba shaguɓe
Ga gungun marassa tarbiya
Yarbawa ku buɗe kunnuwa
Zan ɗan baku saƙo ba yawa
Ku ɗauka ku kai gun ƴan uwa
Musamman na waccan ƙungiya
Mai son yin ƙabilanci yayo
Mai son ɓangaranci je kayo
Kubar masu addini suyo
Shi zai sa a wanye lafiya
Musulmai munason lalama
Idan an riƙe haƙƙin zama
An toshe kafafen gardama
An daƙile ƴan hauragiya
Bama ba asararru kafa
Su suranta aikin Mustafah
Da aikin rago mai jan ƙafa
Bare jaɓa jikan tinkiya
In banda tsiyar ɗan almura
Wa zai auna aikin hijira
Aikin mai ruwan al-kauthara
Da Sunday Igboho mujiya
OPC kuna tono tsiya
Haƙiƙa kunason turjiya
Idan munyi wa zai sha wuya
A faɗin ƙasar Najeriya?!
Shiko tsula jikan ja'ira
Mai ɗakin jarida kafira
Sahara Reporters munkira
Sowore mijin tantiriya
Ya ɗauko batun ya fallasa
Don raini da hangen ya isa
Burinsa ya zamto ƴan ƙasa
Sun harzuƙa ba mai juriya
In har cin mutunci zakuyi
Da dukkan rashin kunya kuyi
Amma kar ku sanyo dausayi
Fiyayyen halitta bai ɗaya
Mai neman ƙasar Ododuwa
Ga fili isasshe mai yawa
Doki zaka hau kayi sukuwa
Ƴanci naka ne in ka iya
Sam-sam babu mai cewa bari
In zaka iya kayi hanzari
Kuje ƙungiya kuyi shawari
Ku samar da hanya bai ɗaya
Yarbawa musamman kafirai
Da ma tawagar Inyamurai
Da duk maguzawa munkirai
Makwautanmu ƴan Najeriya
A kul karku ƙyale karnuka
Su furta miyagun zantuka
Idan kukayo aiki daka
Ƙarshe zaku afka rijiya
Ba mai sha idan munyo fushi
Mu turmutsa hancin ɗan fashi
Bare ja'iri mai jan ƙashi
Da baison a zauna lafiya
┈┉┅━❀🍃🌺🍃❀━┅┉┈
✍🏻
༻📜༺
Abul-Mustapha Al-athary
═══ ༻🕸️༺═══
18/12/1442 🔄 28/7/2021
Ku kasance tare damu a :
👇🏻
👇🏻
👇🏻
Telegram:
https://t.me/alatharytv
YouTube:
https://www.youtube.com/channel/UCFXgXP3MN525l5h5BKXMusA
Facebook:
https://www.facebook.com/alatharytv/
Website:
http://alatharytv.blogspot.com
Call/WhatsApp:
08037894111

Comments
Post a Comment