IDAN ƁERA NADA SATA..
JAGORA DA WANDA AKE JAGORANTA
Allah maɗaukakin sarki ya raba ayyuka kuma yaba kowa nasa:
1- Shuwagabanni su riƙe nasu suyi ƙoƙarin saukewa, domin Allah zai tambayesu game da nauyin da ya dora masu.
2- Waɗanda ake shugabanta suma su riƙe nasu kuma suyi ƙoƙarin saukewa, domin babu shakka za'a tambayesu game da haƙƙoƙin shuwagabanninsu da aka ɗora masu.
Kada wani ya shiga aikin wani!
Duk wanda ya shiga aikin wani, ko yayi sakaci wajen zartar da nasa aikin, lallai ya saɓawa Allah maɗaukakin sarki.
Shugabanci abune mai tsananin wahala, kuma lallai akwai hisabi tsakanin shuwagabanni da mabiya.
Duk wani shugaba wanda yayi amfani da jagorancinsa ko ƙarfin mulkinsa ya muzgunawa waɗanda yake jagoranta, lallai zai tarar da hukuncinsa a wajen ubangijinsa.
Tabbas haƙƙi ne ga shugaba ya tsarewa al'ummarsa ababe kamar haka:
(1) Rayukansu
(2) Addininsu
(3) Dukiyoyinsu
(4) Hankulansu
(5) Mutuncinsu
Da sauransu.
Haƙiƙa Allah maɗaukakin sarki ya wajabta kyautatawa akan komai, shine ya hukunta jagorancinsu, shine kuma zai bincike su yayi masu hukunci cikin sakancinsu, ko kuma ya saka masu da alkhairi game da jajurcewarsu cikin sauke nauyin da ya rataya masu.
Idan muka waiwaya ɗaya ɓangaren zamu tarar cewa :
Allah maɗaukakin sarki bai sahhalewa wani mabiyi yayi taratsi da fito na fito ga shuwagabanni ba, kuma ko kaɗan bai bada dama ga waɗanda ake jagoranta su zama masu neman haƙƙinsu a wajen jagororinsu ta hanyar bore, nuna isa ko hargowa ga shuwagabanninsu ba
Saidai ya ɗora masu nauye-nauye wajen mu'amalantar shuwagabanninsu kamar haka:
(1) Yi masu ɗa'a cikin dukkanin abinda yake daidai
(2) Haƙuri game da zaluncinsu idan azzalumai ne.
(3) Yin nasiha garesu a boye ta hanyar girmamawa da tausasawa.
(4) Yi masu addu'ar gyaruwa da shiriya da samun nasara a cikin jagorancinsu.
Idan ya zamanto akwai wasu haƙƙoƙinsu da suke ganin jagororinsu sun gaza sauke masu, sai su roƙi Allah ya ƙwato masu haƙƙinsu ta hanyar kyawawan addu'o'i.
Babu shakka akwai buƙatar mu kyautata domin mu sami yardar Allah, mu daure muyi riƙo da tafarki madaidaici domin samun tsira duniya da lahira.
Allah ya datar damu da abinda yake so kuma ya yarda dashi.
✍🏻
Abul-Mustapha Al-athary
June 21, 2020.
Comments
Post a Comment