MARTANI GA KUNGIYAR AFENIFERE DA SAHARA REPORTERS
👇 AMSHI : Sahara Reporters ƴan tsiya Jaridar marassa tarbiya Basa son a zauna lafiya ┈┉┅━❀🍃🌺🍃❀━┅┉┈ Da sunanka Allah kai ɗaya Maƙagi gwani mai duniya Gama da ƙasashen nahiya Damu talikan Najeriya Salati kayo gun Mursali Abinso ga duk mai hankali Ba mai ja dashi sai Jahili Koma baya jikan tinkiya Na ɗau ɗamara in saliɓe Taron kafirai zan kakkaɓe In yo martani ba shaguɓe Ga gungun marassa tarbiya Yarbawa ku buɗe kunnuwa Zan ɗan baku saƙo ba yawa Ku ɗauka ku kai gun ƴan uwa Musamman na waccan ƙungiya Mai son yin ƙabilanci yayo Mai son ɓangaranci je kayo Kubar masu addini suyo Shi zai sa a wanye lafiya Musulmai munason lalama...