DAURE KAZAM NAGARI
Sai nake cewa:
Daure kazam nagari
Mai binciken lamari
In kaji kai nazari
Kafin ka kaiwa gari
Zance cikin garari
Sam kar kasa gishiri
Domin akwai haɗari
Zai kada kai da wuri
Harma ya saka ɓari
Duk masu ma marari
Ko zasu zarce ɗari
Ba mai hanaka jiri
Ko can cikin kabari
Sai an saka ka mari
Daure ka gyara shiri
Domin kazam nagari
____________
✍
Abul-Mustapha Al-athary
(Ambassador)
Comments
Post a Comment