TA'AZIYYAR SHEIKH LUHAYDAAN
Qasidah cikin tsarin :
ARAUSA
•┈┈•┈┈•⊰✿🌺✿⊱•┈┈•┈┈•
Mai taken :
Ta'aziyyar Sheikh Luhaydaan
😭😭😭
(1) Mun zam cikin damuwa ƙwarai da ahzaanu
akan rashin gwarzon malami Luhaydaanu
(2) Wannan da zargin mai zargi baya yin tasiri
akansa balle baƙin hali na fattaanu
(3) Wajen nasiha yana yinta cikin hikima
ya fayyace gaskiya tsantsa ga insaanu
(4) Gwani kafaffe akan bin magabata wajen
riƙo ga Sunnah da bibiya ga Qur'anu
(5) Sam baya yarda da tsunbure cikin manhaji
koko kafar yaɗa ayyuka na shaiɗanu
(6) Ya sami ƙauna da karɓuwa wajen talikai
ba ko kuɗi ba mulki irin na sulɗaanu
(7) Saidai idan rabbi ya soka yakan sanya so
ya kewaye duk mutane da dukan jaanu
(8) Ka duba ilminsa ya karaɗe duk duniya
tamkar ya Malik da Zuhriyyu da Sufyaanu
(9) Samun irin malami kamarsa sai an kula
an sa ma'aunin awo a wanga zamaanu
(10) Gurbinka waƙe bazai toshe kafafensa ba
koda yawan baitukan sun zarce diwaanu
(11) Abinda zai kyautu gunmu addu'ace kawai
mukama roƙo da magiya ga Rahmaanu
(12) Allah kayo gafara gareshi mai nunkuwa
ka kankanre duk kurakurai da isyaanu
(13) Ka karɓi kyawawan ayyukansa sannan kasa
ya sami aljannah mai ƙamshi na rayhaanu
(14) Anan nake miƙa ta'aziya ga dukkan musul-
-man duniya har iyalansa da ikhwaanu
✍🏻
Abul-Mustapha Al-athary
═══ ༻🕸️༺═══
3/6/1443 🔄 6/1/2 022
DOMIN SAMUN AUDIO 👇
https://t.me/alatharytv
| Sheikh Saleh Al-luhaydaan |
جزاكم الله خيرًا على هذا الجهد المبذول.. ورحم الله شيوخنا السلفية رحمة واسعة وحفظ أحياهم وثبتنا وإياهم على الإسلام والسنة يا حي يا قيوم
ReplyDeleteآمين يا رب العالمين.
Deleteما شاء الله بارك الله،أحسن الله إليكم وأجزل ثوابكم