Posts

Showing posts from January, 2022

IDAN ƁERA NADA SATA..

Image
  JAGORA DA WANDA AKE JAGORANTA   Allah maɗaukakin sarki ya raba ayyuka kuma yaba kowa nasa: 1- Shuwagabanni su riƙe nasu suyi ƙoƙarin saukewa, domin Allah zai tambayesu game da nauyin da ya dora masu.  2- Waɗanda ake shugabanta suma su riƙe nasu kuma suyi ƙoƙarin saukewa, domin babu shakka za'a tambayesu game da haƙƙoƙin shuwagabanninsu da aka ɗora masu.  Kada wani ya shiga aikin wani!  Duk wanda ya shiga aikin wani, ko yayi sakaci wajen zartar da nasa aikin, lallai ya saɓawa Allah maɗaukakin sarki. Shugabanci abune mai tsananin wahala, kuma lallai akwai hisabi tsakanin shuwagabanni da mabiya.  Duk wani shugaba wanda yayi amfani da jagorancinsa ko ƙarfin mulkinsa ya muzgunawa waɗanda yake jagoranta, lallai zai tarar da hukuncinsa a wajen ubangijinsa.  Tabbas haƙƙi ne ga shugaba ya tsarewa al'ummarsa ababe kamar haka:   (1) Rayukansu   (2) Addininsu  (3) Dukiyoyinsu  (4) Hankulansu   (5) Mutuncinsu Da sauransu. ...

KU YAƊA ALKHAIRI A TSAKANINKU

Image
  LALLAI KUYI UMARNI DA KYAKKYAWA DA KUMA HANI DAGA MUMMUNA  Wajibi ne ga duk wani musulmi wanda ya sami dama da iko, yayi umarni da kyakkyawa da hani daga mummuna musamman ga abinda ya bayyana gareshi. Lallai akwai buƙatar ya natsu cikin hakan wajen amfani da ƙa'idoji da matakai na shari'ah, wato kamar: - ILIMI  - HAQURI  - TAUSASAWA GWARGWADON IKO  - JURIYA GA CUTARWA  - LURA DA MASLAHA DA KISHIYARTA  Da sauransu.  Duk waɗannan zasu afkune sakamakon faɗin ma'aiki-tsira da aminci su ƙara tabbata gareshi-inda yake cewa-: “ DUK WANDA YAGA WANI ABIN ƘI DAGA CIKINKU TO YA CANZASHI DA HANNUNSA, IDAN BAZAI IYA BA SAI YA CANZA DA BAKINSA, IDAN BAZAI IYA BA SAI YA KYAMACESHI DA ZUCIYARSA, WANNAN SHINE MAFI RAUNIN IMANI ” Allah ya bamu ikon fa'idantuwa daga matakan, da kuma ikon gudanar dasu. ✍🏻  Abul-Mustapha Al-athary  June 11, 2015

TA'AZIYYAR SHEIKH LUHAYDAAN

Image
Qasidah cikin tsarin :                   ARAUSA         •┈┈•┈┈•⊰✿🌺✿⊱•┈┈•┈┈•    Mai taken :     Ta'aziyyar Sheikh Luhaydaan                             😭😭😭 (1) Mun zam cikin damuwa ƙwarai da  ahzaanu         akan rashin gwarzon malami Luhaydaanu (2) Wannan da zargin mai zargi baya yin tasiri        akansa balle baƙin hali na fattaanu (3) Wajen nasiha yana yinta cikin hikima        ya fayyace gaskiya tsantsa ga insaanu (4) Gwani kafaffe akan bin magabata wajen        riƙo ga Sunnah da bibiya ga Qur'anu (5) Sam baya yarda da tsunbure cikin manhaji         koko kafar yaɗa ayyuka na shaiɗanu  (6) Ya sami ƙauna da karɓuwa wajen talikai         ba ko kuɗi ba mulki irin na sulɗaanu  (7)...